Gwamnati Za Ta Fara Gwajin Shan Miyagun Kwayoyi Ga Daliban Jami’o’i

0
12

Gwamnatin Tarayya ta amince da shirin fara gwajin gano masu amfani da miyagun kwayoyi a cikin jami’o’i da sauran manyan makarantu a Najeriya.

 Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan bayan ganawa da Shugaban Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA, Janar Buba Marwa (mai ritaya).

A cewar su, gwajin zai shafi sabbin ɗalibai da waɗanda ke ci gaba da karatu, tare da gwaji na bazata domin rage yawaitar shaye-shaye a cikin makarantu. Haka kuma, za a sauya tsarin karatun sakandare domin saka darussa kan illar amfani da kwayoyi.

Janar Marwa ya bayyana cewa sama da mutane 40,000 aka kama bisa laifin ta’ammali kwayoyi, inda aka kwace tan 5,500 na miyagun kwayoyi cikin shekaru biyu. Ya ce shaye-shaye na da alaka da laifukan ta’addanci, fashi da sauran miyagun ayyuka.

Ministan Ilimi ya ce idan matasa suka fada cikin shaye-shaye, ba za su iya karatu da fahimta ba, kuma hakan na hana su samun ilimi mai amfani da aiki a gaba. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here