Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP, yana mai cewa ya daina hulɗa da jam’iyyar a dukkan matakai.
A cikin wata wasika da aka sanya kwanan watan ranar 4 ga Yuli, 2025, wacce aka aikawa Shugaban PDP na Gunduma ta 1 da ke Aiyetoro Gbede a Karamar Hukumar Ijumu ta Jihar Kogi, Melaye, ya bayyana rashin jin daɗinsa da yadda jam’iyyar ke tafiya.
Ya ce ya yanke shawarar ficewar bayan dogon nazari kan halin da jam’iyyar ke ciki, inda ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da halartar harkokin jam’iyyar ba, domin hakan ba zai dace dashi ba.
Melaye ya ƙara da cewa PDP ta nuna gazawa wajen jajircewar da ake bukata domin fitar da Najeriya daga halin da ya kira “lalacewar siyasa” da ke addabar a’lumma.