Karamin Ministan Gidaje, Hon. Yusuf Abdullahi Ata Fagge, ya bayyana cewa a Jam’iyyar APC suna fatan Sanata Barau Jibrin ne zai tsaya takarar kujerar Gwamnan Jihar Kano a zaɓen 2027.
Yayin wata hira da ya yi da Gidan Rediyon Freedom, Ata Fagge ya bayyana cewa babu sabani tsakanin Sanata Barau da Murtala Sule Garo, wanda hakan yasa suke maraba da Murtala ya tsaya takarar Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa karkashin inuwar APC.
A cewar Ata Fagge, tsohon ɗan takarar gwamnan Kano a zaben 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, ma na iya fitowa da niyyar tsayawa takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a 2027. Sai dai ya jaddada cewa kowanne ɗan jam’iyya na da ‘yancin tsayawa takara.
“Mu dai Barau muke goyon baya lokaci ne ya yi da zai jagoranci Kano,” in ji Ata Fagge.