Ba zamu janye yajin aiki ba, sai an biya mana buƙatun mu–Ma’aikatan jinya

0
19

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan jinya ta ƙasa, Morakinyo-Olajide Rilwan, ya bayyana cewa mambobin ƙungiyarsa za su ci gaba da yajin aiki har sai gwamnatin tarayya ta cika dukkanin buƙatun da suka gabatar mata.

Ƙungiyar ta fara yajin aikin gargaɗi na tsawon kwanaki bakwai a faɗin ƙasa daga ranar Laraba, duk da cewa an yi wani zama tsakaninta da Ministan Ƙwadago kafin a fara yajin.

A wata hira da gidan talabijin na Channels, Rilwan ya ce ƙungiyar ba za ta saurari kiran janye yajin aiki daga kowane ɓangare ba matuƙar gwamnati ba ta ɗauki mataki kan matsalolin da suka jima suna fama da su ba.

Ga wasu daga cikin manyan buƙatun ƙungiyar:

A gyara alawus na aikin dare domin daidaita shi da wahalhalun da suke fuskanta;

A ƙara alawus na tufafin aiki da suke sakawa a asibitoci;

A samar da tsarin albashi na musamman da ya bambanta na ma’aikatan jinya da na sauran ma’aikata;

A ƙara musu alawus na ƙarin aiki bayan lokacin da aka tsara;

A ɗauki sabbin ma’aikatan jinya don rage cunkoso da ƙarancin ma’aikata a asibitoci;

Gwamnati ta buɗe wani ɓangare na musamman a Ma’aikatar Lafiya domin kula da sha’anin ma’aikatan jinya kai tsaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here