An gurfanar da ɗan sandan bogi a Kano

0
19

Kotun Majistare ta lamba 24 da ke Kano ta tura wasu maza biyu zuwa gidan gyaran hali bisa zargin su da tayar da zaune tsaye a unguwar Ja’en, cikin karamar hukumar Gwale.

Daya daga cikin mutanen, Usman Isa wanda aka fi sani da Bawan Allah, ana zarginsa da yin karya da sunan jami’in ‘yan sandan sarauniya domin yaudarar jama’a da cin zarafin su.

Shi da abokin laifinsa, Umar Tijjani daga Unguwar Bello a Dorayi Karama, sun gurfana a gaban kotu bisa zargin haɗin baki wajen aikata laifi, shiga gidajen jama’a ba tare da izini ba, sata da kuma lalata dukiyoyi.

Lauyan gwamnati, Barrister Muhammad Bello, ne ya gabatar da ƙarar, inda duka wanda ake tuhuma suka amsa laifin da ake tuhumar su da shi.

Alkalin kotun, Mustapha Abba Dandago, ya bayar da umarnin a tsare su a gidan gyaran hali, sannan ya dage hukunci har zuwa ranar 29 ga watan Agusta, 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here