Za’a kammala titin jirgin ƙasa Kaduna zuwa Kano a 2026–Gwamnatin Tarayya

0
20

Gwamnatin Tarayya ta ce aikin titin jirgin ƙasa daga Kaduna zuwa Kano zai kammala a shekarar 2026.

 Ministan Sufuri, Sa’idu Alkali, ne ya bayyana hakan yana mai cewa lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki, aikin bai wuce kashi 15 cikin 100 ba, amma yanzu an kammala sama da rabin aikin.

Haka zalika, Gwamnatin ta ce ta samu kuɗin gina sabon layin dogo daga Maiduguri zuwa Aba, mai tsawon kilomita 1,443, wanda zai ratsa jihohi takwas. 

Duk da haka, ba a bayyana yadda aka samo kuɗin aikin ba.

Ministan ya ƙara da cewa an kammala gyaran layin dogo na dakon kaya daga Legas zuwa Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here