‘Yan Bindiga Sun Tarwatsa Kauyuka 10 a Katsina, Sama da Mutane 6,000 Sun Yi Gudun Hijira

0
12

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Bakori a jihar Katsina sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kai hari a kauyuka sama da 10, inda suka kashe mutane, suka sace wasu, sannan suka tilasta wa dubban mazauna yankin yin gudun hijira.

Kauyukan da abin ya fi shafa sun haɗa da Guga, Kandarawa, Kakumi, Monono, Ɗan Marka, Sabon Gida, Doma, da ’Yar Dabaru. Harin ya tilastawa fiye da mutane 3,500 yin hijira zuwa cikin garin Bakori, yayin da 2,500 ke neman mafaka a garin Guga.

Mafi yawan waɗanda suka tsere mata ne da yara ƙanana. Wasu sun fake a makarantu da gidajen ‘yan uwa. Shaidun gani da ido sunce an kashe mutane da dama, yayin da wasu suka tsira da rauni.

Wata mace daga kauyan ’Yar Dabaru, Malama Marawiya, ta ce ’yan bindigar sun sace mata fiye da 10, tare da bukatar Naira miliyan 1.5 a matsayin kuɗin fansa kan kowanne mutum.

Shugaban kwamitin kula da ’yan gudun hijira na Bakori, Mamman Yaro, ya ce yawan yan hijira na ƙaruwa kullum, yayin da aka fara raba masu abinci da tallafi daga gwamnatin ƙaramar hukuma.

Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun kafa sansaninsu a dazukan Guga, Kandarawa da Kakumi, inda suke ci gaba da kai farmaki ba kakkautawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here