Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya fitar da sabon hasashen da ke nuna ƙaruwar ci gaban tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2025 da 2026.
A sabon rahoton da IMF ya fitar a watan Yuli, ta ƙiyasta cewa tattalin arzikin Najeriya zai bunƙasa da kashi 3.4 cikin 100 a shekarar 2025, wanda ya fi hasashen da ta yi a watan Afrilu na kashi 3.0.
Har ila yau, IMF na hasashen cewa tattalin arzikin zai ci gaba da bunƙasa da kashi 3.2 a shekarar 2026, fiye da kashi 2.7 da ta yi hasashe a baya.
Wannan sabon hasashe na nuna yuwuwar samun ci gaba a bangaren tattalin arziki a nan gaba, duk da ƙalubalen da ƴan Najeriya ke fuskanta a tattalin arziki da hauhawar farashin kayayyakin masarufi.