Shugaban Hukumar Zaɓe ta Bauchi, Ahmad Makama, Ya Rasu

0
14

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Jihar Bauchi (BASIEC), Alhaji Ahmad Makama Hardawa, ya rasu a ranar Talata, a birnin tarayya Abuja, bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Marigayin ya taba zama Kwamishinan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a jihohin Taraba da Nasarawa, inda ya shafe shekaru yana ba da gudunmawa a harkokin zaɓe a ƙasar nan.

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ne ya bayyana rasuwar cikin alhini da jimami, ta bakin mai magana da yawunsa, Mukhtar Gidado.

A cewar gwamnan, Makama mutum ne mai gaskiya, riƙon amana da ƙaunar ƙasa, wanda ya gudanar da muhimman ayyuka a BASIEC cikin gaskiya da adalci, sannan ya taimaka matuƙa wajen ciyar da dimokuraɗiyya gaba a jihar Bauchi.

Ya ce biyayyarsa ga doka da oda da kuma halayyarsa ta mutunci da ƙwarewa sun ba shi girmamawa daga abokan aiki da jama’ar Bauchi baki ɗaya.

Gwamna Bala ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, ’yan uwansa, abokansa da kuma al’ummar masarautun Hardawa da Misau, yana roƙon Allah Ya gafarta masa, Ya jikansa, ya kuma sanya shi cikin Aljanna Firdaus.

Rahotanni sun nuna cewa aikin ƙarshe da marigayin ya jagoranta a matsayin shugaban BASIEC shi ne zaɓen cike gurbi na shugabancin ƙaramar hukumar Shira da mataimakinsa, wanda aka gudanar a ranar 24 ga watan Mayu, 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here