Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya ce ya haƙo rijiyoyin mai guda huɗu a yankin Kolmani da ke Jihar Bauchi.
Shugaban wani sashin kamfanin, Yusuf Usman, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin taron tattaunawa na kwanaki biyu kan hulɗar gwamnati da jama’a, wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna.
Usman ya ce NNPCL na ci gaba da jajircewa wajen haƙowa da habaka albarkatun mai da iskar gas a yankin Arewa da ma sauran sassan ƙasar nan.
A cewarsa, a wani ɓangare na goyon bayan shirin Shugaba Bola Tinubu na amfani da iskar gas (CNG), ana gina matatun CNG da iskar gas zuwa (LNG) guda biyar a Jihar Kogi.
“Wannan na daga cikin matakan da za su taimaka wajen samar da iskar gas da kuma sauƙaƙa samun ta a fadin yankin Arewa,” in ji shi.