Mai bawa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaron ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa yanzu jama’a za su iya bin hanyar Abuja-Kaduna da dare ba tare da fargaba ba, saboda jami’an tsaro sun kawar da ‘yan ta’addan da suka addabi hanyar.
Ribadu ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin wani taron tattaunawa tsakanin gwamnati da jama’a wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello (SABMF) ta shirya a Kaduna. Ya ce dukkan jami’an gwamnati da ministoci da suka halarci taron sun tafi Kaduna a mota da daddare.a
Ya ce, sakamakon ƙoƙarin jami’an tsaro, hanyar Abuja-Kaduna da ta dade tana fama da matsalar tsaro yanzu ta zama lafiya.
Ya ce ‘yan ta’adda sun yi ƙoƙarin kai hari a kan jirgin ƙasa na Abuja-Kaduna sau da dama, amma jami’an tsaro sun hana hakan cimma nasara.
“Muna iya yin tafiya daga Abuja zuwa Kaduna da dare yanzu saboda mun kashe wadancan miyagun ƴan ta’adda, wato Kachalla Boka, Dogo Isah da Kachalla Shekau, wanda su ne ke da iko da waɗancan yankunan, amma mun kashe su,” in ji Ribadu.
“Bama son yin surutu, amma ‘yan ta’addan da suka kai hari kan jirgin ƙasa sun sake yin ƙoƙarin kai hari sau biyu zuwa uku a wannan gwamnatin, amma mun dakatar da su.
“Babu shakka siyasa ba za ta bar wasu su yaba mana ba, amma ba damuwa. ‘Yan Najeriya za su fahimta. Arewa za ta ji canji. Al’amura na sauyawa, a cewar Ribadu.