Majalisa na binciken Naira triliyan 210 da aka rasa kamfanin mai na ƙasa NNPCL

0
15

Kwamitin bincike na Majalisar Dattawa ya umurci Kamfanin Mai na Ƙasa (NNPCL) da ya bayar da cikakken bayani kan yadda aka yi amfani da kudin da suka kai Naira tiriliyan 210 daga shekarar 2017 zuwa 2023.

Shugaban kwamitin dake binciken yadda NNPCL yayi amfani da kuɗaɗen, Sanata Ahmed Wadada Aliyu daga jihar Nasarawa, ne ya sanar da hakan yayin zaman kwamitin da ya gudana a ranar Talata, inda shugaban kamfanin na ƙasa, Bayo Ojulari, ya bayyana a gaban ‘yan majalisar bayan rashin halartar kiran farko da aka yi masa.

Sanata Wadada ya jaddada cewa dole ne kamfanin ya bayyana yadda kudaden suka salwanta, yana mai cewa babu wani boye boye da za’a yi a cikin wannan binciken.

Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari, ya roƙi afuwa tare da neman karin lokaci, yana mai bayyana cewa mai jima da zama shugaban kamfanin ba.

A cewarsa: “Ina da fiye da tuhuma 19 da nake bukatar lokaci domin nazari da fahimta. Ban dade da kama aiki a matsayin shugaba ba – kusan kwanaki 100 kacal – kuma har yanzu ina tattara bayanai da fahimtar wasu muhimman abubuwa da suka gabata.”

Ojulari ya buƙaci a ba shi makonni hudu, amma kwamitin ya tsaya kan mako uku don mika cikakken bayani kan kudaden.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here