Mai baws shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya bukaci ƴan bindigar da ke addabar arewacin Najeriya da su ajiye makamansu su miƙa wuya.
A wata hira da ya yi da BBC, Ribadu ya ce gwamnatin Tinubu ta samu nasarori a yaki da ta’addanci, inda ya bayyana cewa sun kashe fiye da shugabanni 300 na kungiyoyin ta’adda, kuma yanzu mutane sun fara komawa gonakinsu cikin kwanciyar hankali.
Sai dai, ya amince cewa har yanzu akwai hare-hare a wasu sassan, musamman a Zamfara, Benue, Filato da arewa maso gabas, inda Boko Haram ke ci gaba da haifar da barazana.