Sam Altman, wanda ya kafa kamfanin da ya samar da ChatGPT, ya ja hankalin mutane da su guji bayyana bayanan sirri ga manhajar.
A cewarsa, mutane da dama na raba muhimman sirrika da ChatGPT ba tare da sanin cewa ana iya amfani da irin wadannan bayanai a gaban kotu ba.
Altman ya bayyana hakan a matsayin “babbar matsala”, yana kuma kira ga masu haÉ“aka fasahar su Æ™ara Æ™aimi wajen kare sirrin masu amfani da su.
A gaskiya, fasahar AI tana da iya sauraro sosai, amma ba ta da ikon riƙe sirri. Don haka, yana da muhimmanci mutum ya yi taka-tsantsan da irin bayanan da yake rabawa da irin wannan manhaja. Kada ka saki jiki da yawa, inji Sam.