Wasu mazauna birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun rasa matsugunansu sakamakon ambaliya da aka samu a yau Laraba bayan ruwan sama mai ƙarfi da ya ɗauki sama da sa’o’i uku yana zuba.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin waɗanda ambaliyar ta shafa a unguwannin Damboa Road, Moduganari, Ngomari da wasu wurare sun bar gidajensu domin neman mafaka wurin dangi da abokai.
Wani mazaunin Damboa Road, ya shaida cewa suna fargabar samun karin ambaliya duba da yadda damina ke ci gaba da zub da ruwa.
“A da, idan ruwan sama ya zubo, ruwa kan taru a wuri guda kawai, amma na yau ya bamu mamaki domin ba daga kogi ko wata ma’ajiyar ruwa ya zo ba,” in ji shi.
A unguwar Moduganari, wani mai suna Joshua Solomon ya tabbatar da cewa gidaje da dama sun sun rushe sanadiyar ruwan.
Haka kuma, wata majiya daga gwamnati ta bayyana cewa cibiyar kula da lafiya ta Ngomari itama ta fuskanci ambaliya.