Ƴan Kasuwa Sun Saukar da Farashin Fetur fiye da Na Matatar Dangote

0
19
Man fetur a Najeriya

Masu shigo da man fetur daga ƙasashen waje sun rage farashin lita fiye da na Matatar Man Dangote, lamarin da ke haifar da sabuwar gasa a kasuwar mai.

 Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ke kira ga Gwamnatin Tarayya da ta haramta shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

Rahotanni sun nuna cewa wasu gidajen mai yanzu suna sayar da fetur ƙasa da ₦860 a lita, yayin da abokan huldar Dangote irin su MRS, Heyden da wasu ke sayar da litar tsakanin ₦865 da ₦875 a jihohin Lagos da Ogun.

Wani gidan mai mai suna SGR da ke jihar Ogun ya saukar da farashinsa zuwa ₦847 a lita daga ranar Talata. Wasu ‘yan kasuwa sun tabbatar wa da jaridar The PUNCH cewa yawancin masu shigo da fetur sun karya farashin sayarwa daga wuraren ajiya fiye da na Matatar Dangote.

A ranar Talata, an gano cewa Matatar Dangote na sayar da fetur a ₦820 a lita, yayin da wasu manyan rumbunan ajiya ke sayarwa a ₦815. Shafin dake bayyana farashin mai a kasar nan wato Petroleumprice.ng ya bayyana cewa kamfanoni irin su Aiteo da Menj suna sayar da litar a ₦815.

Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙungiyar dillalan mai masu zaman kansu ta Ƙasa (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya tabbatar da cewa akwai sauyin farashi daga masu shigo da fetur.

“Masu rike da rumbunan ajiya sun saukar da farashinsu. Wasu suna sayarwa a ₦815, wasu a ₦817, yayin da Dangote ke sayarwa a ₦820. Har yanzu NNPC na sayarwa a ₦825, bai saukar da farashinsa ba,” in ji Ukadike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here