Gwamnan jihar Gombe kuma shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya, Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa yankin arewa a shirye yake ya marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a wa’adin mulki na biyu a 2027, duba da yadda gwamnatin sa ke cika alkawuran da ta dauka ga yankin.
Gwamna Yahaya ya bayyana hakan ne a wajen wani taro na kwanaki biyu da Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello (SABMF) ta shirya a Arewa House da ke Kaduna, domin karfafa hulɗar gwamnati da ‘yan ƙasa.
Shugaba Tinubu bai samu halartar taron ba, sai dai ya samu wakilcin Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq da Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris.
Gwamna Yahaya ya ce goyon bayan da yankin arewa ya bai wa Tinubu a zaben 2023 ya kasance mataki mai zurfi na siyasa wanda ke haifar da romon dimokuraɗiyya a fannoni da dama kamar ababen more rayuwa, tsaro, makamashi da noma.
Arewa ta amince da hangen nesan Shugaba Tinubu, ta kuma kada masa ƙuri’a a 2023, inda ta bayar da sama da kaso 60 cikin 100 na ƙuri’un da ya ci nasara da su,” in ji Yahaya.
A cewarsa, duk da ƙalubalen tattalin arziƙi da tsaro da ƙasar ke fuskanta, gwamnatin Tinubu na samun ci gaba mai ma’ana akan su.
Ya ce a zaben 2027, ya kamata a sake bai wa Tinubu goyon baya saboda ya cancanta da hakan bisa ayyukan da ya gudanar da kuma ƙoƙarinsa.