Sojojin Najeriya Sun Daƙile Harin ƴan Ta’adda a Gwoza, Jihar Borno

0
12
Sojoji
Sojoji

Rundunar Sojin ƙasa ta bayyana cewa dakarunta da ke ƙarƙashin Operation HADIN KAI sun samu nasarar daƙile wani mummunan hari da mayakan ƙungiyoyin JAS da ISWAP suka kai a garin Bitta, da ke cikin ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno.

A cewar sanarwar da rundunar ta fitar a shafinta na X, maharan sun iso daga yankin Damboa da nufin kutsawa cikin sansanin sojoji. Sun yi nasarar shiga wani ɓangare na sansanin na ɗan lokaci, amma sojoji sun yi gaggawar fatattakar su bayan musayar wuta mai tsanani.

Rundunar ta bayyana cewa an kashe wasu daga cikin ƴan ta’addan tare da ƙwato bindigogi kirar AK-47 daga hannunsu. Ta ƙara da cewa babu wani soja da ya mutu ko ya ji rauni a harin.

A ranar 28 ga Yuli, 2025, muƙaddashin kwamandan rundunar tare da wasu manyan hafsoshi sun kai ziyara garin Bitta don tantance halin da ake ciki da kuma ƙarfafa gwiwar dakarun da ke bakin aiki.

Rundunar ta bayyana cewa a halin yanzu, al’amura sun fara dawowa dai-dai, duk da cewa har yanzu ana ci gaba da sanya ido kan tsaron yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here