Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata, Ali Modu Sheriff, ya bayyana cewa shi ne ya fara bawa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, damar shiga siyasa, bayan ya ɗauko shi daga aikin banki.
Sanata Sheriff ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, inda ya ce Shettima ya fara siyasarsa ta hannunsa.
A cewarsa: “Allah ne Ya yi ta sanadina Kashim ya shiga siyasa.
Tun yana aiki a banki na kawo shi, na ba shi mukamin kwamishina a ma’aikatu daban-daban. Daga bisani, lokacin da Boko Haram suka kashe ɗan takararmu, sai na ba shi tikitin takara, kuma Allah Ya ba shi nasara, inji Sheriff.
Ba zan bayyana komai akan kokari ko rashin kokarin Shettima a kujerar mataimakin shugaban ƙasa ba, saboda Tinubu ne ya zabo shi don yayi aiki tare da shi, bani da hannu a nan wajen, a cewar Sheriff.