Manoma Sun Kuka Kan Shigo da Shinkafa da Masara Daga Kasashen Waje

0
8

Kungiyar manoman Najeriya ta bayyana damuwa kan yadda shinkafa da masara daga ƙasashen waje ke mamaye kasuwannin cikin gida, abin da suka ce na barazana ga noma, musamman a Arewa.

Manoman sun zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu da ƙirƙirar wata manufa da ke cutar da masu noma, bayan da gwamnati ta sauƙaƙa haraji kan shigo da kayan abinci na tsawon kwanaki 150. Sun ce hakan ya janyo faduwar farashi, wanda ke rage ribarsu kuma yana hana su kwarin gwiwar ci gaba da noma.

Bincike ya nuna cewa buhun shinkafa mai kilo 50 yana kaiwa tsakanin ₦65,000 zuwa ₦68,000, yayin da masara ke kaiwa ₦35,000 zuwa ₦37,000. Duk da haka, shinkafa daga waje na iya kaiwa har ₦83,000.

Tashin farashin taki ya ƙara dagula lamura ga manoma, yayin da masana ke jan hankalin gwamnati ta sake duba wannan manufa domin kare harkar noma a cikin gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here