Kungiyar lauyoyi ‘yan asalin Jihar Kano ta yi kira ga Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya soke nadin da aka yi na mukaddashin shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Kano (PCACC), wanda suka bayyana a matsayin wani matakin da ya saɓawa doka.
A cikin wata takarda da Ismail Haruna, Esq, ya sanya wa hannu a madadin kungiyar, lauyoyin sun bayyana damuwarsu kan yadda wani jami’i da ake kira Alhaji Dauda, wanda ake zargin yana aiki ƙarƙashin tsohon shugaban hukumar, Hon. Muhuyi Magaji Rimin Kano, ya ɗauki matakin sanar da nadin sabon shugaba ba tare da bin ƙa’idar doka ba.
Kungiyar ta jaddada cewa doka ta bayyana karara cewa ikon naɗa shugaban hukumar na hannun gwamna ne kawai, ta hanyar ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), ba wani ma’aikaci ko shugaban wani sashi ba.
Alhaji Dauda, ba shi da wani matsayi da doka ta tanada wanda zai ba shi damar yin sanarwar irin wannan nadin. Wannan lamari ya sabawa dokokin jihar Kano da tsarin mulki,” in ji takardar da kungiyar ta fitar.
Lauyoyin sun gargadi cewa duk wani yunƙurin karɓar iko ba tare da bin doka ba, yana iya haifar da tangarda ga sahihancin aiki da amintar da jama’a ga hukumomin gwamnati. Sun kuma bayyana cewa hukumar PCACC na buƙatar kasancewa a matsayin abar koyi wajen bin doka da gaskiya, ba wurin biyan buƙatun wasu mutane ko ƙungiyoyi ba.
Kungiyar ta gabatar da wasu muhimman bukatu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf kamar haka:
1. A soke nadin da aka yi, wanda ta bayyana a matsayin ba bisa doka ba.
2. A fitar da sanarwa daga ofishin sakataren Gwamnatin Kano SSG, wadda ke fayyace matakan doka na naɗa shugabannin hukumomi.
3. A ɗauki matakin ladabtarwa kan duk wanda ya karya doka ko ya ƙoƙarta karɓe ikon gwamnati ba bisa ka’ida ba.
Lauyoyin sun kumaa jaddada goyon bayansu ga gwamnan Kano, wajen tabbatar da doka da gaskiya a tafiyar da mulki, tare da fatan cewa tarihi zai nuna cewa wannan gwamnati ta tsaya tsayin daka wajen adalci da gaskiya.