Farashin gidan haya ya ninka sau uku a ƙwaryar birnin Kaduna

0
15

Mazauna birnin Kaduna sun koka kan yadda farashin haya ke ƙaruwa da fiye da kashi 150 cikin ɗari a cikin shekara gudFarashin gidan haya ya ninka sau uku a ƙwaryar birnin Kaduna, tare da roƙon Gwamna Uba Sani da ya sa baki kan lamarin.

Wasu mazaunan birnin sun bayyana cewa masu gidaje na ƙara kuɗin haya ba tare da wani dalili ko gyara ba, wasu ma sun ninka kuɗin haya sau uku. Wani mazaunin Unguwan Rimi ya ce baya yana biyan Naira 350,000, yanzu ya koma Naira 900,000 cikin shekara guda.

Sun bukaci gwamnati ta samar da doka da zata kayyade yadda ake ƙara haya, da kuma bada damar biyan haya ta wata-wata ko kowane wata uku.

Sai dai wasu masu gidaje sun ce hauhawar farashin kayan gini da gyara ne ya sa suke ƙara kuɗin haya, duk da cewa suna fuskantar ƙalubale su ma.

Masana sun jaddada cewa akwai buƙatar dokar haya a jihar Kaduna da zata kare haƙƙin masu haya da masu gidaje, tare da samar da tsarin sasanta tsakaninsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here