Babu gwamnan da zai ƙalubalanci sake zaɓar Tinubu–Gwamnan Kaduna

0
51

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa zai yi wuya wani gwamna a Najeriya ya ƙi goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekara ta 2027.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen buɗe taron kwanaki biyu na tattaunawa tsakanin gwamnati da al’umma, wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello (SABMF) ta shirya a Arewa House da ke Kaduna.Ya ce, a tarihi, babu wani shugaban ƙasa da ya nuna cikakken goyon baya ga gwamnoni da gwamnatocin jihohi kamar yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi a yanzu.

Gwamna Uba Sani ya ƙara da cewa saboda haka, da wuya a samu wani gwamna a ƙasar nan da zai tsaya ya ƙalubalanci shugaban ƙasa.“Karon farko a tarihin Najeriya ake gudanar da tattaunawa da waɗanda ba gwamnati ba don tantance matsaloli da lalubo hanyoyin ci gaba a arewa” in ji shi.

Ya ce wannan sabon salo na gudanar da harkokin ƙasa na nuni da yadda abubuwa ke sauyawa wajen magance matsalolin da suka addabi ƙasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here