Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya karrama ‘yan wasan Super Falcons da dukkan ma’aikatan tawagar da lambar girmamawa ta (OON), saboda nasarorin da suka samu.
Shugaban ya kuma ware musu gidaje masu dakuna uku a Abuja.
Baya ga hakan, ya ba da umarnin bayar da kyautar kuɗi mai tsoka, inda kowane ɗan wasa zai samu $100,000 (kimanin Naira miliyan 150), yayin da kowanne daga cikin mambobin kwamitin gudanarwar tawagar 11 zai karɓi $50,000 (kimanin Naira miliyan 75).
Wannan karramawar ta gudana ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, a wani taron musamman da aka shirya domin girmama Super Falcons.
Bugu da ƙari, kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta hannun shugabanta kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman AbdulRasaq, ta bai wa kowanne ɗan tawagar kyautar Naira miliyan goma (₦10,000,000).