Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana watsi da yankin Arewa wajen aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa.
A wata hira da aka yi da shi a Trust TV, Lawal ya ce babu wani aikin gwamnati da ke bayyane a Arewa, yana mai cewa duk mai hangen nesa zai fahimci yankin na fuskantar wariya.
Ya goyi bayan kalaman tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Kwankwaso, wanda ya ce gwamnatin Tinubu na mayar da hankali ne kan wani yanki guda, sannan tana barin wasu a baya.
Lawal ya kuma nuna shakku kan makomar APC a Arewa, yana mai cewa jam’iyyar ba za ta iya samun nasara a zaben gaba ba idan har ta ci gaba da wannan salon mulki.
Sai dai Ministan Ayyuka, David Umahi, da mai ba shugaban ƙasa shawara kan kafafen yada labarai, Sunday Dare, sun musanta zargin, inda suka ce akwai manyan ayyuka fiye da 40 da ake aiwatarwa a Arewa a halin yanzu.