Super Falcons Sun Dawo Gida Zasu Gana da Tinubu

0
13

Ƴan wasan ƙwallon ƙafa na mata na Najeriya, Super Falcons, sun iso gida Najeriya bayan nasarar da suka samu a wasan ƙarshe da suka doke Maroko a birnin Rabat na ƙasar Morocco, gasar cin kofin Afrika ta mata a ranar Alhamis.

An tarbi tawagar a filin jirgin saman Abuja, inda jami’an gwamnati suka nuna musu girmamawa. 

Ana sa ran za su gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa daga bisani a yammacin yau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here