Jam’iyyar SDP ta sanar da korar tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, tare da haramta masa duk wata hulɗa da jam’iyyar na tsawon shekaru 30.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Araba Aiyenigba, ya fitar a Abuja, jam’iyyar ta ce El-Rufai bai taɓa yin rijista da ita ba a matakin mazaɓa, kamar yadda kundin tsarin mulkin ta ya tanada.
SDP ta zargi El-Rufai da yin ikirarin zama membanta a kafafen sada zumunta, tare da ƙirƙirar takardu na bogi domin tabbatar da hakan. Haka kuma, an ce yana yunkurin rikita lamuran cikin gida na jam’iyyar, da yada bayanan ƙarya da kuma yunƙurin jefa SDP cikin haɗin gwiwar siyasa ba bisa ƙa’ida ba tare da jam’iyyar ADC.
Saboda haka, SDP ta umarci Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) da sauran hukumomi da su guji ɗaukar El-Rufai a matsayin memban jam’iyyar, tare da haramta masa amfani da sunan SDP, alamar jam’iyyar, ko halartar duk wani taron da ya shafi jam’iyyar.
Sanarwar ta ƙara da cewa daga yanzu har zuwa shekaru 30 masu zuwa, El-Rufai ba shi da izinin sake neman zama memba ko wakiltar jam’iyyar ta kowace hanya.