Hukumar kula da yanayi ta ƙasa (NiMet) ta yi hasashen samun ruwan sama mai haɗe da iska, tare da yiwuwar ambaliya a wasu yankuna daga yau Litinin zuwa Laraba.
A cewar sanarwar da NIMET ta fitar ranar Lahadi a Abuja, za a samu guguwar iska da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a safiyar Litinin a jihohin Jigawa, Zamfara, Kano, Kaduna, Bauchi, Yobe da Katsina. Daga bisani kuma za a ci gaba da samun ruwan sama a waɗannan yankuna da ƙarin jihohin Kebbi, Adamawa da Taraba.
NiMet ta yi gargaɗin yiwuwar ambaliya musamman a wasu sassan jihohin Bauchi, Jigawa, Katsina, Kaduna da Kano.
A yankin tsakiyar ƙasar ƙasar nan kuwa, za a fara da samun gajimare da ruwan sama a wasu sassa kamar su Neja, Binuwai, Abuja, Filato da Nasarawa, daga bisani, za a samu karin ruwan sama a ƙarin wasu jihohi.
Yankin kudu kuwa zai fara da gajimare, sai kuma a sami ruwan sama mara karfi zuwa matsakaici a yankunan Ondo, Imo, Abia, Enugu, Ebonyi, Anambra, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom.
A ranar Talata da Laraba, NiMet ta ce za a ci gaba da samun ruwan sama da guguwar iska a jihohin arewa da tsakiya da kuma kudu, tare da gargaɗin yiwuwar ambaliya a wasu sassa, musamman a jihar Filato.