NIMC da EFCC Sun Gargadi ‘Yan Najeriya Kan Sayar da Lambar NIN akan Naira 1500

0
7

Hukumar dake bayar da lambar shaidar zama ɗan ƙasa NIMC ta gargadi ‘yan Najeriya da su daina sayar da Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN) da bayanansu na sirri don wasu ‘yan kudi kamar ₦1,500, tana mai cewa hakan na barazana ga tsaron kasa da sirrin mai lambar.

EFCC ta bayyana cewa wasu matasa na biyan mutane ₦1,500 zuwa ₦2,000 domin su karɓi bayanan NIN ɗin su, sannan su siyar da su ga kamfanonin Fintech har ₦5,000.

NIMC ta ce ba za ta ɗauki alhakin duk wani bayani da mutum ya bayar da kansa ba. Ta kuma bukaci a’lumma su riƙa amfani da manhajar NINAuth App don kare bayanansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here