KACCIMA Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni

0
10

Cibiyar Kasuwanci, Masana’antu, Ma’adinai da Aikin Gona ta Kano (KACCIMA) ta zaɓi Ambasada Usman Hassan Darma a matsayin sabon shugabanta, bayan zaben da ya kawo ƙarshen rikicin shugabancin da ya ɗauki kusan shekaru biyar, na faruwa a cibiyar.

A jawabinsa, Darma ya ce jagorancin sa zai mayar da hankali kan samar da sauye-sauye, a cibiyar ƙarfafa ƙwarewar mambobi da haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki domin haɓaka tattalin arzikin Kano.

 Ya kuma bayyana cewa za su tafiyar da aiki cikin gaskiya da haɗin kai ga kowa.

Tsohon shugaban cibiyar, Garba Imam, ya ce sun gina tubali mai ƙarfi wanda ya kafa KACCIMA a matsayin cibiyar kasuwanci ta zamani mai ɗorewa, tare da sauye-sauyen da suka haɗa da inganta tsarin aiki da walwalar ma’aikata.

Sabbin Shugabannin KACCIMA sun haɗa da:

1. Shugaba: Amb. Usman Hassan Darma

2. Mataimakin Shugaba na 1: Abdulaziz Sabitu Mohammad

3. Mataimakin Shugaba na 2: Umar Ismail Haruna

4. Mataimakin Shugaba (Ma’adinai): — ba’a bayyana suna ba

5. Mataimakin Shugaba (Masana’antu): Kabir Mohammed Adamu

6. Mataimakiyar Shugaba (Yaɗa Labarai): Sameera Abubakar Abdullahi

7. Mataimakiyar Shugaba (Kamfanoni): Binta Muhammad Jibrin

8. Mataimakin Shugaba (Gidaje): Aliyu Mustapha Mohammed

9. Mataimakin Shugaba (Kasuwanci): Nura Habibu

10. Ma’aji: Umar Ladiyo Ibrahim

11. Mataimakin Shugaba (Aikin Gona): Yusuf Aliyu Umar

12. Mataimakiyar Ma’ajiya: Aisha Sulaiman Baffa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here