Jihar Lagos zata fuskanci ɗaukewar wutar lantarki mai tsawo

0
10
wutar lantarki

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na ƙasa (TCN) ya sanar da fara wani muhimmin gyara a layin wutar lantarki daya taso daga Omotosho zuwa Ikeja West a jihar Legas, wanda zai fara daga Litinin, 28 ga Yuli, zuwa 21 ga Agusta, 2025.

Sanarwar ta bayyana cewa aikin zai gudana daga ƙarfe 8 na safe zuwa 5 na yamma a kowace rana, kuma an samu amincewar Hukumar Kula da Harkokin Wuta ta Ƙasa (NERC) da Hukumar Tsarin Rarraba Wuta ta Ƙasa (NISO).

Shugabar hulɗa da jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ta ce bayan kammala aikin kowace rana, za a dawo da wuta ta wannan layi, yayin da sauran layuka za su ci gaba da aiki don rage tasirin katsewar wutar.

Kamfanonin rarraba wuta na Eko da Ikeja sun gargadi abokan huldarsu da su shirya fuskantar katsewar wutar akai-akai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here