Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da shirin sake buɗe wasu cibiyoyi guda biyar da za’a yi amfani dasu wajen horas da mutane 1,400 a sana’o’in dogaro da Kai a fannoni daban-daban.
Cibiyoyin da za a buɗe sun haɗa da:
- Cibiyar Koyar da Kiwon Kaji da ke Tukui (karamar hukumar Makoda) – za ta horas da mata 600 a kiwon kaji.
- Cibiyar Gyaran Hali da ke Kiru, zata koyar da ɗinki, walda, gyaran kwamfuta da wayar hannu ga mutane 200
- Cibiyar Koyar da Sana’ar Kamun Kifi da ke karamar hukumar Kabo zata koyar da dabarun kamun kifi ga mutane 200.
- Cibiyar Koyar da Noman Rani da ke Gwarzo, zata horar da (mutane 200
- Cibiyar Koyon Aikin Jarida, zata horar da mutane 200.
Wannan mataki na daga cikin yunkurin gwamna Abba, na farfaɗo da cibiyoyin koyon sana’o’i guda 26 da aka kafa a zamanin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda suka lalace daga baya.
Shugaban Hukumar Kididdiga ta Jihar Kano, Dokta Aliyu Isa, ya bayyana cewa an kammala dukkan shirye-shirye na buɗe cibiyoyin, ciki har da kayan koyarwa, abinci, da kayan aiki.
Ya ƙara da cewa gwamnati na da ƙudurin bai wa masu cin gajiyar shirin horo mai nagarta tare da cikakken tallafi domin samun nasarar kammala karatunsu cikin sauƙi.