Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa fiye da mutane miliyan 1.2 na fama da ciwon hanta nau’in Hepatitis B a jihar.
Kwamishinan lafiya, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana hakan a yayin bikin Ranar Hepatitis ta Duniya ta 2025, inda ya bayyana cutar a matsayin babban barazana ga lafiyar jama’a, duk da cewa anayin rigakafin cutar.
A matsayin mataki na dakile yaduwar cutar, gwamnati ta fitar da Naira miliyan 95 domin shirin “HepFree Uwadajariri”, wanda ke nufin dakatar da yaduwar cutar daga uwa zuwa jariri. Ana bawa mata masu juna biyu magani kyauta, tare da rigakafin gaggawa ga jarirai bayan haihuwa, inji shi.
Kwamishinan ya ce kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na kamuwa da cutar a Najeriya na faruwa ne daga uwa zuwa jariri. Don haka, gwamnatin jihar ta gabatar da buƙatar ƙarin Naira miliyan 135 domin faɗaɗa shirin zuwa asibitoci da dama.