An kwashe namun dajin gidan tsohon Akanta na Ƙasa, zuwa gidan Zoo a Kano

0
11

An kwashe namun dajin gidan tsohon Akanta na Ƙasa, zuwa gidan Zoo a Kano

Shugaban gidan gidan adana namun daji na Kano, Sadik Kura Muhammad, ya tabbatar da cewa an kama babban maciji nau’in python da ya tsere daga gidan tsohon Akanta Janar na Ƙasa, Ahmed Idris, inda aka mayar da shi tare da wasu namun daji zuwa gidan adana namun dajin Kano.

Ɓacewar macijin ya tayar da hankula a unguwannin Daneji da kewaye a jihar Kano. Daga cikin sauran namun daji da aka gano a gidan Idris akwai kada da kuma ƙaramin damisa.

Maƙwabtan yankunan Daneji, Mandawari, Kabara da Soron Dinki sun bayyana cewa sun kasa samun natsuwa har sai da aka kama macijin aka fitar da shi daga yankin.

A wata hira da ya yi da gidan rediyo a Kano, Sadik Kura Muhammad, ya ce bayan fargaba da tashin hankali da lamarin ya jawo, tsohon Akanta Janar ɗin da kansa ya mika duka namun dajin dake gidan sa zuwa gidan Zoo, inda ake tsare da su yanzu.

Muhammad ya bayyana cewa Idris na da lasisin da ya halatta masa riƙe irin waɗannan namun daji a gidansa, kuma ba su kai wani mataki da za su zama barazana ba.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar da cewa an fara bincike kan lamarin, kuma an gayyaci Ahmed Idris domin amsa tambayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here