Amurka Zata Hana Ƴan Najeriya Zuwa Kasar Don Haihuwa

0
25

Gwamnatin Amurka ta fitar da sabon gargaɗi ga ƴan Najeriya dangane da neman izinin shiga ƙasar domin haihuwa kawai.

A wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar a shafinsa na X, a yau Litinin, an bayyana cewa duk wani mai neman biza da aka gano cewa tafiyarsa na da nufin haihuwa ne domin jaririn da za a haifa ya samu takardar zama ɗan ƙasar Amurka, to za a hana shi damar shiga ƙasar.

Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an bayar da biza za su ƙi amincewa da irin waɗannan buƙatu, musamman idan an fahimci cewa babban dalilin tafiyar mutum shi ne haihuwa a Amurka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here