Ƴan Bindiga Sun kashe mutane 38 bayan karɓar Miliyan 50 a Zamfara

0
10

Mutane 38 ne suka rasa rayukansu a ƙauyen Banga da ke ƙaramar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara, duk da cewa an biya kuɗin fansar su har naira miliyan 50 ga ‘yan bindigar da suka sace su.

Shugaban ƙaramar hukumar Kaura Namoda, Mannir Haidara Kaura, ya shaida wa Channels TV cewa ‘yan bindigar sun sace mutum 56, amma daga baya suka saki 18 kacal. Wadanda aka sako an kwantar da su a asibiti sakamakon azabar da suka sha a hannun masu garkuwar.

Kaura ya ce gwamnatin jihar ta na shirin kai ziyara domin jajantawa ga iyalan mamatan da lamarin ya shafa.

A cewar wani mazaunin ƙauyen, Ibrahim Banga, ‘yan bindigar sun kai hari watanni baya inda suka sace mutane 53, sannan suka buƙaci a biya Naira miliyan ɗaya kan kowane mutum.

Ya ce bayan dogon lokaci da wahala, al’ummar ƙauyen suka tattara kuɗin suka kai wa ‘yan bindigar, amma abin takaici mutum 18 ne kawai aka sako.

“Da suka dawo, sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yanka sauran mutum 35 ɗin ɗaya bayan ɗaya,” in ji Banga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here