‘Yan Sandan Jigawa Sun Kama Masu Safarar Makamai
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Jigawa ta kama mutum biyu da ake zargi da safarar makamai tare da kwato bindigu biyu ƙirar gida.
DSP Lawan Shi’isu, mai magana da yawun rundunar, ya ce jami’ai sun kama Abdussamad Haruna mai shekara 30 a Kazaure yayin da yake ƙoƙarin kai bindigar zuwa jihar Filato.
Haka kuma, an kama wani Auwalu Yusuf daga Kano tare da wata bindiga a hannunsa.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Dahiru Muhammad, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin tare da tabbatar da aniyar rundunar wajen kare lafiya da dukiyoyin jama’a.
Rundunar ta kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da ba dawa jami’an tsaro sahihan bayanai domin yaki da aikata laifi.