Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ogun ta tabbatar da kama mutum 21 da ake zargi da kasancewa mambobin wata ƙungiyar asiri, ciki har da sojoji biyu, yayin wani samame da aka kai wani otel da ke birnin Abeokuta.
Kakakin rundunar, SP Omolola Odutola, ta bayyana cewa an gudanar da samamen ne a ranar Juma’a, bisa sahihan bayanan sirri da suka samu dangane da taron da mambobin ƙungiyar Aiye ke shirin yi.
Binciken ya gano bindiga ƙirar gida, gatari, huluna masu launin jini da dama da sauran kayayyakin da ake dangantawa da ayyukan asiri a hannun wadanda ake zargin.
SP Odutola ta ce an riga an miƙa su ga sashen binciken manyan laifuka da ayyukan asiri domin ci gaba da gudanar da cikakken bincike.