NNPP ce jam’iyya mafi ƙarfi a jihar Kano—Kwankwaso

0
10

Tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa na NNPP a 2023, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsu ce mafi karfi a jihar Kano, inda ya bayyana cewa ba za’a iya yin nasara akan Kwankwasiyya ba.

Yayin da yake jawabi a bikin yaye dalibai na Jami’ar Northwest, inda aka bashi digirin girmamawa, Kwankwaso ya jaddada cewa inganta fannin ilimi da ci gaban dan Adam shine ginshikin Kwankwasiyya, wanda hakan ya janyo mata karbuwa a wajen al’umma.

Ya tunatar da al’umma yadda gwamnatinsa ta kafa jami’o’i biyu a Kano tare da tallafa wa dubban matasa su samu karatu a gida da waje, inda da dama daga cikinsu suka zama malamai a manyan makarantu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin farfaɗo da harkar ilimi a jihar da kuma cika burin tafiyar Kwankwasiyya, yana mai bayyana cewa gwamnatinsa ta biya bashin fiye da Naira biliyan 4 a shekaru biyu.

A yayin bikin, wasu manyan ’yan Najeriya da suka hada da marigayi Alhaji Aminu Dantata da Hajiya Mariya Dantata, sun samu digirin girmamawa daga jami’ar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here