Rahotanni daga Yola, babban birnin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar nan, na nuna cewa ambaliyar ruwa ta mamaye wasu unguwanni a yankin.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar na jihar, SP Suleiman Yahaya, ya bayyana cewa unguwannin da lamarin ya fi shafa sun haɗa da Shagari Low Cost, Sabon Pegi, da Modire Yolde Pate, duk a cikin karamar hukumar Yola ta Kudu.
A cewar SP Yahaya, dakarun musamman na rundunar masu ƙwarewa a harkar ceton ruwa sun isa yankunan a cikin jiragen ruwa domin kai agaji da taimakon gaggawa ga al’ummar da abin ya shafa.
Wasu daga cikin hotunan da aka wallafa sun nuna yadda ruwa ya mamaye gidaje, inda a wasu wuraren zurfin ruwan ya kai har rabin tsawon mutum.