Ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa sun bayyana matsananciyar damuwa game da yadda yunwa ke ƙara ta’azzara a arewacin Najeriya, musamman sakamakon raguwar tallafin kuɗi daga ƙasashen waje.
Ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ta bayyana cewa a cikin watanni shida da suka gabata, yara kimanin 600 da suke kula da su a sansanoninta sun rasa rayukansu saboda matsanancin ƙarancin abinci mai gina jiki.
Haka zalika, shirin ciyar da marasa galihu na Majalisar Ɗinkin Duniya, wato World Food Programme (WFP), ya sanar da shirin dakatar da duk wani agaji na abinci da ake bayarwa a yankin arewa maso gabas cikin wata mai zuwa, saboda ƙarancin kuɗaɗen da yake samu.
Rahotanni sun nuna cewa raguwar tallafin kuɗin anda ya fara tun a zamanin mulkin Shugaban Amurka, Donald Trump tare da hauhawar farashin kaya da tashe-tashen hankulan ‘yan ta’adda, ya taimaka matuƙa wajen ƙara tsananta matsalar yunwa a yankin.