Tawagar ‘yan wasan Najeriya ta mata, Super Falcons, ta sake nuna bajinta a gasar cin kofin Afrika ta mata (WAFCON), inda ta lashe kambunta na goma bayan da ta doke kasar Morocco da ci 3-2 a wasan da aka buga daren Asabar.
Wannan nasara ta kara tabbatar da matsayin Super Falcons a matsayin ƙungiyar da ta fi kowacce ƙasa yawan lashe wannan gasa a nahiyar Afrika.