Sulaiman Danwawu ya tsere, ya bar Kwamishinan Sufuri cikin Garari–Daily Nigerian

0
13

Sulaiman Danwawu, da aka ayyana a matsayin shahararren mai safarar miyagun ƙwayoyi da kotun tarayya da ke Kano ta bayar da belinsa kwanan nan, ya tsere, inda ya bar mai tsaya masa har kotu ta bayar da shi beli, wato Kwamishinan Sufuri na jihar Kano, Ibrahim Namadi, cikin garari.

A ranar Alhamis, jaridar DAILY NIGERIAN ta bayar da rahoto kan yadda Kwamishina Namadi ya tsaya wa Danwawu, har kotu ta bayar dashi beli, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga jama’a.

Majiyoyi sun shaida wa jaridar cewa bayan rahoton da ya jawo martani daga jama’a, Kwamishinan ya kira Danwawu, yana roƙon ganin sa cikin gaggawa.

“Da Danwawu ya fahimci yadda jama’a suka fusata da belin da aka ba shi, sai ya kashe wayoyinsa, ya guje wa Kwamishinan, kuma ya ƙi bayyana kansa,” in ji wata majiya.

Biyo bayan bacewar Danwawu, a daren Juma’a Kwamishina Namadi ya fitar da wata sanarwa inda ya janye daga tsaya masa a gaban kotu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here