Shirin Kano-ACReSAL ya karyata wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta da ke zargin rashin gaskiya da gazawa wajen aiwatar ayyukan da shirin ke gudanarwa.
A wata sanarwa da Jami’ar Hulɗa da Jama’a, ta ACReSAL , Maryam Abdulqadir, ta fitar, ta bayyana bidiyon a matsayin ƙoƙarin yaudarar jama’a akan abinda ba gaskiya ba.
Ta ce shirin yana gudana ne bisa yarjejeniya tsakanin Gwamnatin Tarayya, Jihohin Arewa 19 da Abuja da Bankin Duniya, karkashin wasu Æ™a’idojin da aka yiwa laÆ™abi da PIM da PAD.
Shirin ya karyata zargin cewa:
1. Yanaa haƙo rijiyoyin burtsatse na hannu maimakon masu amfani da hasken rana, inda aka tabbatar da cewa an gina rijiyoyin burtsatse masu amfani hasken rana guda 10 a kan ƙa’idojin Bankin Duniya.
2. Zargin cewa KuÉ—aÉ—en tallafawa a’lumma na Community Revolving Fund, ba su kai hannun waÉ—anda aka tsara shirin domin su ba, inda Maryam tace a ranar 6 ga Fabrairu 2025, al’ummomi daga kananan hukumomi huÉ—u sun karÉ“i $250,000 (₦375m) daga Gwamna Abba Kabir Yusuf;
3. Zargin ba a sayi motoci da injinan É—ibar shara ba, inda ta bayyana cewa an riga an sayo motocin 12, kuma suna yin aiki a titunan Kano.
Shirin ya bukaci jama’a da masu wallafa labarai su rika bincike kafin yada bayanai, tare da ziyartar shafin yanar gizo na shirin domin samun sahihan labarai.