Gwamnan Kano ya bayar da umurnin binciken kwamishinan Sufuri kan alaƙar sa mai safarar miyagun ƙwayoyi

0
11

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin da ke nuna cewa Kwamishinan Sufuri na jihar, Alhaji Ibrahim Namadi, yana da hannu a karɓar belin Sulaiman Danwawu, da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi.

Wannan umarni ya biyo bayan yadda al’umma suka da jin labarin cewa daya daga cikin mahukuntan Kano ne yayi belin wanda ake zargin duk da cewa gwamnati na yin kokarin magance al’adar shan miyagun kwayoyi a tsakanin a’lumma.

Mai magana da yawun Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwar daya fitar a safiyar yau Asabar.

Domin warware lamarin, Gwamna Yusuf ya kafa kwamitin bincike na musamman ƙarƙashin jagorancin Barrista Aminu Hussain, wanda shi ne mai ba da shawara na musamman kan harkokin shari’a da kundin tsarin mulki, ga gwamnan.

Kwamitin na da alhakin gano gaskiyar al’amarin da bayar da shawarwari masu gamsarwa nan take.

Mambobin Kwamitin sun haɗa da:

1. Barr. Aminu Hussain – Shugaban Kwamitin

2. Barr. Hamza Haladu – Mamba

3. Barr. Hamza Nuhu Dantani – Mamba

4. Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar – Mamba

5. Manjo Janar Sani Muhammad (Rtd.) – Mamba

6. Kwamared Kabiru Said Dakata – Mamba

7. Hajiya Bilkisu Maimota – Sakatariya

Yayin da yake bayyana kafa kwamitin, Gwamna Yusuf ya nuna matuƙar damuwa da zargin da aka yi, tare da jaddada aniyarsa ta yaki da safarar miyagun kwayoyi da duk wani nau’in aikata laifi a fadin jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here