Aƙalla mutum 15, ciki har da wani jami’in ‘yan sanda, ne suka rasa rayukansu a hare-hare biyu da wasu ‘yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Bokkos da ke Jihar Filato a ranar Alhamis, 24 ga Yuli, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa an kai ɗaya daga cikin hare-haren ne da misalin ƙarfe 4 na yamma, lokacin da mazauna ƙauyen Chirang ke dawowa daga kasuwar Bokkos zuwa ƙauyen Mangor, inda ‘yan bindigar suka afka musu.
Shugaban masu sa ido kan zaman lafiya na ƙaramar hukumar Bokkos, Kefas Mallai, ya tabbatar da cewa mutum 14 ne suka mutu a harin, tare da raunana wasu uku.
A cewarsa, kafin wannan farmaki, an harbe wani ɗan sanda na MOPOL da safe a wani shingen bincike da ke kan hanyar Richa, a wani hari na daban.
Shugaban ƙaramar hukumar, Amalau Amalau, ya bayyana harin a matsayin abin takaici da ke buƙatar gaggawar daukar mataki daga gwamnati. Ya ce an riga an kai gawarwakin da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos.
Kokarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred, bai yi nasara ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.