Kwamishinan harkokin sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Namadi, ya tsaya wa wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi mai suna Suleiman Danwawu, a matsayin wanda zai yi belin sa a gaban kotu.
Alkalin kotun tarayya da ke Kano, Mai shari’a MS Shu’aibu, ya gindaya sharuddan beli masu tsauri ga Danwawu, a ranar 16 ga Yuli, inda ya bukaci a gabatar da kwamishina mai ci a majalisar zartarwar jihar Kano, tare da ajiye Naira miliyan biyar (₦5,000,000).
Sai dai duk da wahalar da ke tattare da samun irin wannan mutum, Kwamishina Namadi ya shigar da takardar rantsuwa da wasika zuwa kotu yana bukatar zama mai tsayawa Danwawu.
Wasikar, wacce jaridar DAILY NIGERIAN, ta samu kwafin ta, an rubuta ta ne a ranar 18 ga Yuli, 2025 zuwa ga mataimakin babban maga takardan kotun tarayya da ke Kano. A cikin wasikar, Namadi ya bayyana shirinsa na tsayawa wa Danwawu don bayar dashi beli.
A wasikar an rubuta cewa, ina rokon izini in tsaya wa wanda ake kara a wannan kara (SULAIMAN AMINU) wanda wannan kotu mai daraja ta bayar da beli a kan kudi Naira miliyan uku (₦3,000,000) da kuma mutum daya da zai tsaya masa tare da ajiyar Naira miliyan biyar (₦5,000,000). Na amince da sharuddan belin kuma zan tabbatar da kawo wanda ake kara a duk ranar da aka dage shari’a har zuwa karshe.”
Lokacin da aka tuntubi Namadi don jin ta bakinsa, ya ce yana cikin taro, kuma zai dawo da kira daga baya. Amma har lokacin da aka kammala rubuta rahoton, bai sake kiran ba.
A ranar 21 ga Mayu, Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta gurfanar da Danwawu a kotun tarayya da ke Kano bisa tuhume-tuhume guda takwas da suka shafi fataucin kwayoyi. Bayan gurfanar da shi a ranar 28 ga Mayu, an dage sauraron bukatar belinsa zuwa 16 ga Yuni, kuma aka tura shi gidan yari.
Sakamakon yadda shari’ar ta dauki hankalin jama’a, reshen kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) na Kano ya bayyana cewa zai sanya ido sosai kan shari’ar Suleiman Danwawu.