Kwamishina Namadi ya janye daga karɓar belin mai safarar miyagun ƙwayoyi 

0
14

A ci gaba da shari’ar da ke gudana tsakanin Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Sulaiman Aminu Danwawu mai safarar miyagun ƙwayoyi mai (lamba: FHC/KN/CR/93/2025), Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Namadi, ya sanar da janye hannunsa matsayin wanda ya tsayawa wanda ake tuhuma don samun beli a gaban kotu.

A cikin wata wasika da ya aike wa Mataimakin maga takardan kotun, Alhaji Namadi ya bayyana cewa ya yanke wannan shawarar saboda dalilai na kashin kansa da kuma bukatar kare mutuncinsa da kuma martabar ofishinsa a matsayin jami’in gwamnati.

Kwamishinan ya bayyana cewa amincewarsa da bayar da beli tun da fari an yi ta ne bisa niyyarsa ta kai-da-kai, bisa tanadin doka, tare da la’akari da dangantaka ta dangi da kuma dalilan jin ƙai tsakanin sa da wanda ake zargi. Ya ce wannan mataki ba ya nufin yana goyon bayan aikata laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi ko kuma yana marawa zargin da ake masa baya.

Alhaji Namadi ya sake jaddada biyayyarsa ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da sauran mambobin majalisar zartarwa ta jihar, da kuma al’ummar Kano gaba ɗaya. Haka kuma ya nuna cewa a shirye yake ya bayar da karin bayani idan akwai buƙata.

Daga ƙarshe, Namadi ya nanata kudurinsa na ci gaba da tallafawa kokarin gwamnati wajen yaki da amfani da miyagun ƙwayoyi da tsaro ga al’ummomin jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here