Faransa Za Ta Amince Da Falasdinu A Matsayin Ƙasa Mai Ƴanci – Macron

0
11

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa ƙasarsa za ta amince da Falasdinu a matsayin ƙasa mai cikakken ‘yanci, a hukumance, a lokacin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya da za a yi a watan Satumba a New York.

Macron ya ce wannan mataki na nuni da burin Faransa na ganin an samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, tare da kawo ƙarshen yakin Gaza da ceto rayuwar fararen hula. Ya ce dole ne a kwance damarar Hamas da sake gina Gaza cikin zaman lafiya da tsaro.

Falasdinawa sun yaba da matakin, yayin da Isra’ila da kawayenta irin su Amurka suka soki shi, suna masu cewa hakan na iya ƙara wa Hamas ƙarfin gwiwa. Fira Ministan Isra’ila Netanyahu ya bayyana cewa Falasdinawa ba zaman lafiya suke so ba, sai dai nufin kawar da Isra’ila.

Yanzu haka, ƙasashe fiye da 140 daga cikin mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya sun riga sun amince da Falasdinu, amma ƙasashe masu tasiri irin su Amurka da Birtaniya har yanzu ba su amince ba.

Tun bayan harin Hamas a watan Oktoba 2023, Isra’ila ta kashe fiye da Falasdinawa 59,000 a Gaza, inda yawancin yankin ya koma lalatacce, kuma yara da dama na fama da yunwa da cututtuka saboda hana kayan agaji shiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here