Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar da martani ga zargin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na cewa gwamnatin Tinubu tana nuna wariya ga Arewa. Kwankwaso ya yi wannan furuci ne a Kano, inda ya ce ana ware albarkatun ƙasa ga Kudu, lamarin da ke ƙara talauci da rashin tsaro a Arewa.
Sai dai mai bawa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ce zargin ba gaskiya ba ne, yana mai cewa gwamnatin Tinubu na aiwatar da muhimman ayyuka a Arewa.
Ya lissafa ayyukan tituna kamar Abuja–Kaduna–Kano, bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano, da kuma gine-ginen asibitoci da cibiyoyin lafiya fiye da 1,000, da yace gwamnatin Tinubu nayi domin Cigaban arewa.
Ya kuma ce akwai shirin noma da ya shafi jihohi tara da kuma ayyukan jirgin ƙasa da makamashi a sassa daban-daban na Arewa.
Dare ya jaddada cewa Arewa na cikin shirin ci gaban gwamnatin Tinubu.